Labarai
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare-haren da ƴan Boko Haram suka kai a garin Darul-Jamal na ƙaramar hukumar Bama da ke jihar Borno, inda aka kashe akalla Mutane 63, ciki har da fararen hula da sojoji, sannan aka ƙone gidaje da sace mutane.
Mai wakiltar Majalisar ta Dinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Fall, ya ce lamarin ya sabawa dokokin kare hakkin ɗan Adam, yana kuma kira ga hukumomin Najeriya su kama waɗanda suka shirya harin su gurfanar da su a gaban shari’a tare da gaggauta sakin mutanen da aka sace.
Ya kuma jaddada cewa Majalisar za ta ci gaba da tallafawa gwamnati wajen kare fararen hula da dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.
You must be logged in to post a comment Login