Labarai
Majalisar datijjai ta amince da tabbatar da nadin manyan alkalan kotun koli
Majalisar datijjai ta amince da tabbatar da nadin manyan alkalan kotun koli su 8.
A dai makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar datijjan wasikar neman sahalewar su kan nada alkalan wanda shugaban majalisar Ahmad Lawan ya karanta a ya yin zaman majalisar a dazun nan.
A cewar wasikar shugaban kasar ya ce nadin ya biyo bayan shawarwarin da majalisar kula da al’amuran shari’a ta kasa ta bayar kan nadin na su.
Wasikar ta shugaban kasa ta bayyana cewar matakin nadin ya yi dai-dai ta sashi na 231 na cikin kundin tsarin mulkin kasar nan na shekara ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima
Daga cikin wadanda aka nada akwai Lawal Garba daga Arewa maso yamma da Hellen Ogunwumiju daga kudu maso yamma da Abdu Aboki daga Arewa maso yamma da kuma M M Saulawa shima daga Arewa maso yamma.
You must be logged in to post a comment Login