Connect with us

Labarai

ACF ta ƙaddamar da kwamitin kula da Asusun tara kuɗaɗen tallafi

Published

on

Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa Arewa ACF, ta ƙaddamar da kwamitin kula da Asusun Tallafi na Naira biliyan 100 domin inganta ilimi da ƙarfafa matasa da bunƙasa tattalin arziki.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da kwamitin, shugaban Kwamitin Amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, ya ce asusun wani muhimmin mataki ne na faɗaɗa damar ilimi da tallafa wa ci gaban al’ummar Arewa.

Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Dahiru Abubakar, da tsohon gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ne za su jagoranci kwamitin da aka ɗora wa alhakin kula da aiwatar da manufofin asusun.

Alhaji Bashir Dalhatu, ya ce, ACF ta ƙaddamar da asusun ne a lokacin bikin cika shekaru 25 da kafuwarta, inda aka samu alƙawarin gudummawar Naira biliyan 7. da miliyan dari 800 daga mutane da ƙungiyoyi, amma zuwa yanzu an karɓi kusan Naira biliyan 3 da miliyan 900 da aka ajiye a Bankin Jaiz.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!