Labarai
Majalisar Dattawa ta dakatar da Tinubu daga tura sojoji kasar Nijar
Yan majalisar dattawan Nijeriya sun yi watsi da bukatar shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman izinin tura dakarun kasar zuwa Jamhuriyar Nijar bayan kungiyar ECOWAS ta ce, za ta yi amfani da karfi domin maido da zababben shugaban kasar da aka yi wa juyin mulki.
‘Yan majalisar sun sanar da matsayarsu ne a wani zama da suka gudanar a a jiya Asabar.
‘Yan Majalisar sun Kuma jinjinawa shugabannin Kungiyar Bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS kan jajircewarsu wajen ganin sun maido da kasar kan tsarin dimokradiyya.
Sai dai sanatocin ba su amince da bukatar daukar matakin soji a kasar ba, saboda alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
A maimakon haka, sanatocin sun bukaci shugaba Tinubu da ya kara kaimi ta fuskar zaman sulhu tare da sojojin da suka hambarar da mulkin shugaba Mohamed Bazoum.
You must be logged in to post a comment Login