Connect with us

Labarai

NSCDC ta kori jami’an sa-kai biyar a Kano saboda rashin ɗa’a

Published

on

Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa (NSCDC) reshen jihar Kano ta kori wasu jami’an sa-kai biyar daga aiki bisa zargin rashin ɗa’a, rashin ƙwarewar aiki da kuma aikata abubuwan da suka saɓa wa ƙa’idojin hukumar.

 

Mai magana da yawun hukumar a Kano, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata. Ya ce kwamandan NSCDC na jihar Kano, Mohammed Hassan Agalama, ya amince da korar jami’an ne bayan an binciki laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

 

Jami’an da aka kora sun haɗa da Yakubu Mubarak Yusuf, Isma’il Muhd, Adamu Auwalu, Abdulrazaq Suleiman da Ahmad Sarki. Hukumar ta ce ta kwace dukkan kayan aiki, kayan sawa da katunan shaidar aiki da suke amfani da su.

 

Kwamandan ya kuma umarci dukkan shugabannin yankuna da na ofisoshin hukumar a faɗin jihar da su tabbatar da cewa ba a sake bai wa waɗanda aka kora wata dama ta wakiltar NSCDC ba. Ya jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci duk wani hali da zai zubar mata da mutunci ba, yana mai cewa duk wanda aka samu da irin waɗannan laifuka zai fuskanci hukuncin da ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!