Labarai
Majalisar dinkin duniya ta bukaci Buhari ya yi amfani da siyasa don shawo kan matsalar tsaro
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da tattaunawa da kuma bin hanyoyin siyasa wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar.
Babban Jakadan Majalisar da ke Najeriya Edward Kallon ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar shugaban, inda ya ke cewa matsalolin tsaron da suka addabi kasar da ke da rassa daban daban na da wahalar magance su.
Kallon ya ce yayin da sojoji su ke can suna fafatawa, yana da matukar muhimmanci a goya musu baya wajen tattaunawa da amfani da hanyar siyasa domin samun zama lafiya.
Jami’in ya bayyana matsalolin da suka addabi Najeriya guda 3 da suka hada da matsalar zama dan kasa da mallakar dukiyar kasa da kuma rikicin shugabanci.
Kallon ya ce Majalisar na kashe akalla Dala biliyan guda da rabi kowacce shekara wajen gudanar da ayyukan jinkai a Najeriya, musamman a yankin da ake fama da rikicin boko haram.
You must be logged in to post a comment Login