Labaran Kano
Majalisar dokokin jiha zata magance matsalolin muhalli
Majalisar dokoki ta bayyana cewa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalolin muhalli a fadin jihar Kano.
Shugaban kwamitin kula da harkokin muhalli na majalisar, wakilin karamar hukumar Takai a majalisar Alhaji Musa Ali Kachako, ya bayyana haka a ziyara zuwa ofishin hukumar aikin dakile zaizayar kasa da ambaliyar Ruwa ta kasa shiyyar Kano.
Musa Ali Kachako, kara da cewa lamarin muhalli abu ne da ya kamata a dube shi da muhimanci tare da bullo da hanyoyin da za a magance matsalar sa.
Karin labarai:
Shin ina makomar matsalar gurbatar muhalli a Jihar Kano
Majalisar zartaswa ta amince da fitar da Naira Miliyan 977don samar wa hukumar fasa kwauri muhalli
A ya yin ziyarar Alh Musa Shuaibu , ya ce gwamnatin tarayya ce ta bayar da aikin tun a shekara ta 2012 da nufin magance matsalar kwararowar Hamada da matsalar zaizayar kasa a fadin kasar nan.
In da yace an kaddamar da aikin ne a nan Kano a shekarar 2017, wanda an samu cigaba kwarai na dashen bishiyu da gina madatsar ruwa da sauran wasu manyan ayyuka, musamman guraren dake fuskantar barazanar Hamada.
Wakilinmu Auwal Hassan Fagge, ya ce Alhaji Musa Shuaibu, ya bukaci da a sakarwa takwarar hukumar ta jihar Kano kudade cikin gaggawa don cigaba da ayyukanta.
You must be logged in to post a comment Login