Jigawa
Majalisar dokokin jihar jigawa ta janye dakatarwar da ta yiwa wakilin Gumel
Majalissar dokokin jihar Jigawa ta janye dakatarawar data yi wa wakilin karamar hukumar Gumel Sani Isya Abubakar.
Shugaban majalissar dokokin jahar Idris Garba Jahun ne ya sanar da haka a yau yayin zaman majalissar.
Kakakin majalisar ya ce an dawo da wakilin ne sakamakon sanya baki da wasu mutane masu kima suka yi daga mazabar dan majalissar.
Majalisar ta dakatar da Sani Isya Abubakar ne kusan wata uku da suka gabata bisa wani dalili da bai bayyana ba.
Idris Garba ya kara da cewa kamar yadda dokar majalissar dokokin Jigawa ta bada dama a dakatar da duk wani Wakili da aka same shi da lefi haka kuma ta bada damar dawo dashi, wadda kuma hakan aka yi bisa rokon wadancan mutane.
Sai dai kafin hakan Sani Isya Abubakar ya shigar da kara gaban kotu bisa zargin majalissar dokokin jihar da shugaban ta da kuma akawun majalissar kan dakatar dashi ba bisa ka ida ba.
Haka kuma yace ba a bashi damar kare kansa ba sannan kuma a bakin mutane yaji an ma dakatar dashi, domin har kawo yau ba a fada masa laifin da yayi ba, wato dai yana nufin ba a bashi a rubuce ba, wadda yace wadannan matakai ne da ake bi, kafin daukar irin wannan mataki.
Haka kuma ya yi zargin ba a shigar da batun gaban kwamatin da’a na majalissar ba, balle ayi bincike har kwamati ya tura rahoto gaban majalissa, kafin daukar matakin dakatarawa ko akasin haka.
You must be logged in to post a comment Login