Labarai
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar gwajin jini kafin aure
Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.
Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar Dokokin jahar kano Alh. Jibril Ismail Falgore ya ce dokar za ta dakile yaduwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yada su ga iyali da al’umma.
Dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu hadari da wuyar magani kafin yin aure tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda ya ki biyayya ga dokar.
Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alh. Nasiru Magaji ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita.
You must be logged in to post a comment Login