Labarai
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta amince da sabuwar dokar ma’adanai
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta amince da sabuwar dokar hakar ma’adanai a Jihar, wadda ta ba da damar haka tare da karbar kudaden haraji daga masu hakar ma’adanan.
Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoton da kwamitin harkokin kudi da tsare-tsare na majalisar ya yi a zamanta na jiya alhamis.
Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin Alhaji Sama’ila Salihu Biu, ya ce, kafin gabatar da rahoton sai da suka tattauna da masu ruwa da tsaki da lamarin ya shafa, tare da fito da shawarwari da al’amuran da ya kamata a yi wa duba na tsanaki musamman a harkokin karbar haraji.
Dokar dai ta yi tanadin cewa, dukkan wuraren hakar ma’adanan za su kasance karkashin mallakin gwamnatin jihar, don haka gwamnatin jihar na da ikon karbar kudaden haraji daga masu hakar ma’adanai.
You must be logged in to post a comment Login