Connect with us

Labarai

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Rogo da Ɓagwai da Bebeji

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Rogo da Ɓagwai da kuma Bebeji na tsawon watanni uku.

 

Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan da ta ce, ta same su badaƙalar kuɗi.

 

Haka kuma, umarci mataimakan su da su ci gaba da jagorantar tafiyar da kananan hukumomin.

 

Wannnan dai na zuwa ne bayan gabatar da rahoton da Kwamitin majalisar na ƙananan hukumomi da masarautu, inda ya ce, ya karɓi korafe-korafen mutane da wasu daga cikin majalisun kansilolin ƙananan hukumomin kan zarge-zargen da ake musu.

 

Shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Alhaji Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, Dr. Alhassan Salisu na Bebeji da Alhaji Abubakar Mustapha Rogo na Rogo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!