Labarai
Mazauna Darazo su 10 sun rasu sakamakon hatsarin mota
Mutane 10 ‘yan asalin Ƙaramar Hukumar Darazo ta Jihar Bauchi suka rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyar zuwa Bauchi.
Hakan na kunshe a cikin sanarwar ta’aziyyar da Ofishin Dan Majalisar Tarayya na Darazo da Ganjuwa Mansur Manu Soro, ya fitar.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Darazo ya kai ziyara Asibitin Koyarwa na Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin duba lafiyar waɗanda suka jikkata tare da jajanta wa iyalan mamatan.
Tuni aka gudanar da jana’izar mutane biyar daga cikin waɗanda suka rasu.

You must be logged in to post a comment Login