Labarai
JNPSNC ta buƙaci Minista Oyedele ya kira taron gaggawa jinkirin biyan albashi da tallafi

Majalisar Tattaunawar ƙungiyoyin ƙwadago,ta Najeriya JNPSNC, ta buƙaci Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, da ya kira taron gaggawa domin tattauna jinkirin biyan albashi da ƙarin tallafi na watanni biyu da kuma fara aiwatar da alawus na musamman na kaso 40 cikin 100 ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Ƙungiyar ta ce tana son ganawa da ministan kafin ko a ranar 11 ga Agustan 2026, tana mai gargaɗin cewa idan ba a warware matsalolin ba, hakan na iya haifar da rashin kwanciyar hankali tsakanin ma’aikatan gwamnati.
A cikin wasiƙar da aka aike wa ministan, wadda Sakataren Ƙasa na majalisar, Gbenga Olowoyo, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ƙasa, Benjamin Yanto, ƙungiyar ta nuna takaicinta cewa wasiƙu biyu da ta aika a baya kan batun ba su samu amsa ba.
JNPSNC ta bayyana cewa manufar taron ita ce a samo mafita cikin lumana ga buƙatun jin daɗin ma’aikata da har yanzu ba a biya ba, tare da kauce wa abin da ta kira rikicin ƙwadago da ke ƙara ƙamari.
Ƙungiyar ta ce tana sa ran taron zai magance matsalolin da suka rage domin hana tashin hankali da kuma rikicin ƙwadago.
Haka kuma, ta jaddada cewa ya kamata a biya bashin ƙarin albashin watannin Maris da Afrilu tare da albashin ma’aikata na waɗannan watanni.
You must be logged in to post a comment Login