Addini
Majalisar Shari’ar Musulunci ta naɗa Dr Bashir Aliyu a matsayin shugabanta

Majalisar Shari’ar Musulunci ta kasa, ta naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba mai dauke da sa hannun sakataren majalisar Nafiu Baba Ahmed, ta ce, an amince da shuagabancin Dakta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugabanta.
A ranar Litinin ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu a jihar Osun da ke kudancin Najeriya ya na da shekara 81 a duniya.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa, za a sanar da sabon mataimakin shugaban majalisar a nan gaba.
Sheikh Dakta Bashir Aliyu Umar sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Kano.
You must be logged in to post a comment Login