Labarai
Majalisar wakilai ta dage dawo wa ci gaba da ayyukanta
Majalisar wakilan Nijeriya ta sanar da dage koma wa domin ci gaba da zamanta zuwa ranar 30 ga watan Janairun bana.
Hakan na kunshe ne ta cikin wani sako da mai tsawatarwa na majalisar Yahaya Danzaria, ya aikewa yan majalisar,
Sanarwar ta ce, yana mai cewa za a koma zaman majalisar ne a ranar 30 ga watan Janairu da misalin karfe 11:00 na safe.
Rahotonni sun bayyana cewa, hakan na zuwa ne makonni biyu da zartar da kasafin kudin bana da majalisun kasar suka yi.
You must be logged in to post a comment Login