Labarai
Majalisar zartarwar Kano ta amince da kashe biliyan tara don gina gadar shataletalen gidan man NNPC
Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da kashe naira biliyan takwas da miliyan dari tara da tamanin da dubu dari uku da uku da dari hudu da sittin da kwabo sittin da uku don gina sabuwar gada mai hawa uku akan titin Maiduguri kusa da gidan mai na NNPC.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano kwamared Muhammed Garba ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da safiyar yau talata.
Ya ce gadar da a turanci ake kira da inter-change an sanya mata sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Malam Muhammed Garba ya kuma ce aikin gadar wani bangare ne na kokarin da gwamnatin Kano ke yi don rage cunkoso a cikin birnin Kano.
Kwamishinan ya kuma ce majalisar zartarwar ta Kano ta kuma amince da ware naira miliyan arba’in da hudu da dubu dari uku don shirin tantance kwasa-kwasai a kwalejin nazarin aikin gona ta Audu Bako da ke Dambatta.
You must be logged in to post a comment Login