Tsaro
Major Janar Taoreed ya shiga ofis a matsayin babban Hafsan sojin kasa na 23
Sabon babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya kama aiki a matasayin babban hafsan sojin ƙasa na 23, inda ya yi alkawarin sauke nauyin da aka ɗora masa bisa adalci.
Lagbaja ya karbi aiki ne a hannun Laftanar Janar. Faruk Yahaya wanda ke kan kujerar tun watan Mayun 2021.
A cewar sa burin kowanne soja shi ne ya samu damar zama shugaban sojoji.
Ya kara da cewa zai yi la’akari da cancanta da aiki tuƙuru tsakanin dakarun sojin Nijeriya, inda ya ce zai kyautata daidai gwargwado tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen dawo da wadanda suka kauce hanya a jagorancinsa.
You must be logged in to post a comment Login