Labarai
Malaman addini a Kano sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya baki kan rikicin Sudan
- Dakta Aliyu Haruna Muhammad ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya baki kan rikicin da ke rafuwa a kasar Sudan
- Shima Malam Abdulmutalib Ahmad ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen kwaso al’ummarta da ke zaune a Sudan
- Bakin biyu sun yi kira ga hukumomi da su yi abinda ya dace
Wani malamin addinin musulunci kuma malami a sashin nazarin addinin musulunci a jami’ar Bayero da ke jihar Kano Dakta Aliyu Haruna Muhammad ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya baki kan rikicin da ke rafuwa a kasar Sudan.
Dakta Aliyu Haruna Muhammad ya bukaci hakan a zantawarsa da Freedom Radio da safiyar yau, wadda tattaunawar ta mayar da hankali kan rikicin da ke faruwa yanzu haka a kasar ta Sudan, wanda ya rutsa da wasu yan Najeriya.
A nasa bangaren Dakta Abdulmutallib Ahmad Muhammad wanda malami ne a kwalejin nazarin addinin musulunci a garin Daura da ke jihar Katsina cewa yayi, ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen kwaso al’ummarta da ke zaune a Sudan kamar yadda sauran kasashen duniya ke kwashe na su.
Bakin biyu sun yi kira ga hukumomi da su yi abinda ya dace, musamman na kwaso yan kasar su daga cikin halin da suke ciki a Sudan, daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin bangarori biyu a kasar.
Rahoton: Nura Bello
You must be logged in to post a comment Login