Labarai
Malaman islamiyya sun yi Alkunutu a Kano
Kungiyar Alarammomi mahaddata Al’kur’ani ta kasa reshen jihar Kano ta gudanar da Alkunutu a wani mataki na janyo hankalin gwamnati don bai wa makarantun allo da islamiyya damar ci gaba da karatu a jihar nan.
Shugaban kungiyar Alarammomi Malam Gwani Sunusi Abubakar ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala sallar ta Alkunutu wadda ta gudana a yau.
Malam Gwani Sunusi yace sun shirya yin Alkunutun ne da nufin zaburar da gwamnati ta duba halin da ilimin addini ya shiga sakamakon dakatar da makarantun sanadiyyar annobar corona, yana mai cewa gwamnati ta bayar da damar bude makarantun islamiya da tsangaya a jihar nan.
Ya Kara da cewa matukar ana son ganin warakar kowacce irin cuta wajibi ne a koma ga Allah ta hanyar bai wa makarantun addini damar ci gaba da ilimantar da yara da sanya su yin addu’o’i ga kasa.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa a yayin Al’kunutun malamai daga sassan jihar Kano daban daban ne suka halarta inda kuma suka gudanar da addu’o’i na musamman ga kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login