Labarai
Mambobin NUT sun dakatar da yajin aikin da suke yi a Abuja

Kungiyar Malaman makaranta ta kasa NUT reshen Babban Birnin Tarayya Abuja ta dakatar da yajin aikin malaman firamare da sakandare nan take, bayan taron gaggawa da aka gudanar domin nazarin shiga tsakani da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi a rikicin da ya fara ranar 20 ga Afrilun nan da muke ciki.
Shugaban kungiyar, Abdullahi Shafa, ya ce ministan ya amince da ware naira biliyan 5 duk wata domin biyan bukatun malamai, inda biliyan 2 za su fito daga kudaden shiga na Abuja, sannan biliyan 3 daga kaso 10 cikin 100 na kudaden shiga da kananan hukumomi ke samu, domin biyan alawus na musamman na kashi 40 da sauran hakkoki.
Kungiyar ta umurci dukkan malamai su koma bakin aiki ranar Litinin 27 ga Afrilu, tare da gargadin cewa kada a hukunta wani malami saboda shiga yajin aikin. Ta kuma ce za ta sake duba matsayarta idan gwamnatin Abuja ba ta cika alkawuran da ta dauka ba.
You must be logged in to post a comment Login