Labarai
Mambobin PDP na Kudu maso Gabas na iya ficewa matukar ta gaza amincewa da Sunday Udeh-Okoye

Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya ce, mambobin jam’iyyar adawa ta PDP daga yankin Kudu maso Gabashin kasar na iya ficewa daga cikin jam’iyyar matukar jam’iyyar ta gaza amincewa da Sunday Udeh-Okoye a matsayin sabon sakataren ƙasa.
Gwamna Mbah ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi yayin da yake ganawa da manema labarai bayan wani taron sirri da wasu manyan shugabannin PDP daga Kudu maso Gabas suka yi a fadar gwamnatin jihar Enugu.
Cikin manyan shugabannin jam’iyyar da suka halarci taron akwai Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Adolphus Wabara, da Shugaban jam’iyyar a yankin Kudu maso Gabas, Ali Odefa.
Sauran sun haɗa da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa Okwesilieze Nwodo, da tsohon gwamnan Jihar Ebonyi, Sam Egwu, sai tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Josephine Anenih.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana ci gaba da samun rikici a cikin jam’iyyar tsakanin Samuel Anyanwu da Udeh-Okoye kan wanda ya dace da kujerar sakataren ƙasa na jam’iyyar ta PDP.
You must be logged in to post a comment Login