Labaran Wasanni
Manchester City ta dauki ‘yar wasa Lucy daga Lyon
Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Manchester City ta sake daukar ‘yar wasan kasar Ingila, Lucy Bronze daga kungiyar Lyon.
Lucy Bronze ta saka hannu a kwantiragin shekara 2 da Manchester City.
‘Yar wasan, mai shekaru 28, ta yi nasarar lashe gasar Champions League ta mata karo 3 ajere da kungiyar ta Lyon.
You must be logged in to post a comment Login