Labaran Wasanni
Manchester United ta dakatar da sayar da rigar dan wasanta Greenwood ta kafar Internet

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta dakatar da sayar da rigar dan wasan ta Mason Greenwood ta kafar Internet.
United ta dakatar da dan wasan mai shekaru 20 a ranar Lahadi, 30 ga watan Janairu bayan da aka yada hotuna da faifan murya na laifukan da ake zarginsa da shi a shafukan sada zumunta.
An cire rigar Greenwood daga sayar da ita a hada-hadar sayar da kayayyaki ta Internet bayan zargin sa da akayi.
You must be logged in to post a comment Login