Labarai
Manene dalilan da suka sanya Buhari zuwa kasar Mali
A yau Alhamis ne ake sa ran cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar gida Najeriya don tattaunawa kan batun sasanta rikici tsakanin ‘yan adawa da shugaban kasar Mali.
A dai shekaran jiya ne tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan ya yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan da kungiyar ECOWAS ta nada shi ya jagoranci kwamtin sasanta rikici tsakanin shugaban kasar Mali Boubacar Keita da ‘yan adawa.
Daga cikin shugabanin kasashen Afrika ta yamma da ake kyautata zaton za su halaci taron akwai Alassane Outtara na Cote d’Ivoire da Nana Akufo Addo Ghana da na Senegal Macky Sall
Wannan na kunshe cikin sanarwar da mashawarcin shugaban kasa kan kafafan yada labarai Femi Adesina ya sanyawa hannu wacce jaridar Punch ta wallafa a jiya.
Shugaban jamhuriyyar Niger Issoufou Mahamadou ya amince su hado a Bamako babban birnin kasar don tattuna batun sasatan rikicin siyasa da ya kunnu kai a kasar ta Mali.
You must be logged in to post a comment Login