Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Maniyyata aikin Hajjin bana su fara shiri – NAHCON

Published

on

Hukumar jindaɗin Alhazai ta jihar Kano ta ce, hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa NAHCON ta sanar da ita cewa a bana za’a gudanar da aikin hajji.

Babban Sakataren hukumar Malam Muhammad Abba Ɗambatta ne ya sanar da hakan a yayin taron manema labarai da safiyar ranar Litinin.

Malam Muhammad Abba Ɗambatta ya ce hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa, NAHCON, ta umarci hukumomin jindaɗin alhazai na jihohi da su yi maza-aza su fara shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2022 bayan da hukumar ta samu tabbaci daga hukumar kula da aikin hajji da umara ta ƙasar Saudiya.

Da yake amsa tambayoyi ga manema labarai Dambatta ya ce, “A baya ƙasar Saudiya ta dakatar da ƙasashe 18 daga shiga cikinta ciki har da Najeriya a sakamakon ci gaba da bazuwar annobar covid-19”.

Yanzu haka dai ministan cikin gida na ƙasar Saudiyya ya aiko mana takarda cewa ƙasar ta cire dukkan wasu takunkumai da ya danganci annobar covid-19” a cewar Ɗanbatta.

Ɗanbatta ya kuma ce “Maniyyatan da suka bar kuɗaɗen su tun a shekara ta 2020 da kuma 2021 su ne mutanan farko da za mu fara tantancewa domin su tafi aikin a kan lokaci, kuma idan mutum yana buƙatar karɓar kuɗinsa har yanzu ƙofa a buɗe take”.

Wakilin Freedom Radio Bilal Nasidi Mu’azu ya rawaito cewa, hukumar ta kuma ce da zarar an sanar da adadin kujerun da za’a baiwa Najeriya hukumar za ta sanarwa maniyata halin da ake ciki.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!