Addini
Maniyyata Hajjin bana sun yi dafifi a filin Arfa don gudanar da Ibadu

A yau Alhamis ne Alhazai daga sassa daban-daban na duniya suka hallara a Dutsen Arafat na kasar Saudiyya domin gudanar da ibadar wuni guda wadda ke guda daga cikin rukunan aikin Hajji.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa, ranar Arafat, ita ce ranar tara ga watan Zul-Hijja wadda muhimmiyar rana ce a aikin Hajji da kalandar Musulunci.
A Ranar ne miliyoyin alhazai ke hallara a Dutsen Arafat da ke kusa da Makka don gudanar da rukunin aikin Hajji mafi muhimmanci da aka fi sani da Wuqoof-e-Arafa.
Ana kuma ruwaito cewa Dutsen Arafat shi ne wurin da Annabi Muhammad SAW, ya gabatar da jawabinsa na karshe wanda aka fi sani da hudubar bankwana shekaru 1,435 da suka gabata.
Ana daukar ranar a matsayin kololuwar aikin Hajji, inda alhazai ke shafe tsawon yini suna gudanar da addu’o’i.
Haka kuma Ita ce, ranar da musulmin da ba sa aikin Hajji ke yin Azumin neman lada da kankare zunubansu da neman gafarar Allah.
You must be logged in to post a comment Login