Labarai
Manyan kotunan jihar Kano za su fara hutun su na shekara-shekara
Manyan kotunan jihar Kano za su fara hutun su na shekara-shekara.
Mai magana da yawun kotun Kano Baba Jbo Ibrahim ne ya bayyana hakan, ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Freedom Radio.
Baba Jibo ya ce, hutun na su zai fara a ranar 23 ga watan da muke ciki kuma zai ƙare a ranar 3 ga watan Oktoba na wannan shekara.
“La’akari da doka ta kundin tsarin babbar kotun jihar kano ta shekarar 2021, wadda ta bai wa babban jojin Kano mai shari’a Nura Sagir Umar dama na bai wa manyan kutanan hutu” inji Baba Jibo.
Mai magana da yawun kotunan ya kuma ce” an samar da wasu alƙalai na shirin ko-ta-kwana da suka haɗar da babban jojin Kano mai shari’a Nura Sagir Ibrahim da mai shari’a Dije Abdu Aboki sai Sunusi Ado Ma’aji da za su zauna a kotuna yayin wannan hutu” cewar Baba Jibo.
Baba Jibo Ibrhaim ya ce, ana sanar da dukkanin lauyoyin gwamnati da masu zaman kan su, har ma da masu shigar da ƙara da su san da wannan hutu.
You must be logged in to post a comment Login