Labaran Wasanni
Manyan labaran wasanni a Najeriya
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta yi barazanar janye kwantaraginta da kocin Super Eagles Gernot Rohr matsawar kungiyar ta gaza tabuka rawar gani.
Ministan wasanni, Sunday Dare, ne ya bayyana yayin wata hira ad aka yi da shi a gidan talibijin na kasa.
A ranar 27 ga watan Mayun 2020 hukumar NFF ta tsawaita kwantaragin mai horas da Super Eagles Gernot Rohr tsawon shekaru biyu wanda zai kaishi zuwa 31 ga watan Disambar 2022.
Ministan wasannin na Najeriya ya ce yana fatan Gernot Rohr, zai yi rawar gani don ganin Super Eagles din ta samu gurbi a gasar cin kofin Duniya da za a yi a kasar Qatar a shekarar 2022.
Hukumar NFF dai na fatan Super Eagles din karkashin jagorancin Gernot Rohr za ta yi dukkan mai yuwuwa don ta lashe gasar cin kofin Afrika da shima zai gudana a shekarar 2021 a kasar Kamaru.
Ko da yake, a baya Gernot Rohr, ya ce yana da yakinin Super Eagles zata lashe gasar cin kofin Afrika da aka yi a kasar Masar, sai dai hakan be samu ba, haka kuma ya sha alwashin zai kai Najeriya zuwa ga gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Qatar a 2022.
You must be logged in to post a comment Login