Labarai
Manyan laifukan da ake zargin Ibrahim Magu
Tun farkon nadin Ibrahim Magu a matsayin mukaddashin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC wasu na ganin cewa bai can-canci rike mukamin ba, la’akari da rahoton rashin can-canta game dashi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayar tun a wancan lokacin.
Haka ma dai aka yi ta dambarwa a majalisar dattijai bayan da aka mika sunan Ibrahim Magu, inda ‘yan majalisu suka ki amincewa dashi, sai dai fadar shugaban kasa ta tsaya kai da fata akan ganin an tabbatar dashi a mukamin, wanda a yanzu kuma ake ganin sun raba hannun riga.
Yanzu dai ana zargin Ibrahim Magu da aikata wasu manyan laifuka, wadanda sukayi sanadiyyar tunbike shi daga kujerar, wadannan laifuka kuwa sune:
1. Yiwa ministan shari’a tsageranci
2. Sace kudaden da aka kwato daga wadanda ake zargi
3. Sayar da kadarorin da aka kwato daga wadanda ake zargi, ko kuma sayarwa da ‘yan lelensa.
4. Son kai wajen bayar da ayyukan binciken laifuka ga ma’aikatan hukumar ta EFCC
5. Fitar da bayanan sirri ga wasu kafafan yada labarai da yake da ya zaba.
Yanzu haka dai tuni binciken kwamitin fadar shugaban kasa yayi nisa, wanda har rahotonni ke cewa anje har gidan Magun an kuma bincika ko ina, sai dai har zuwa yanzu kwamitin bai bayyana sakamakon abinda ya riska a gidan Magun ba.
labarai masu alaka :
Gambari ya gana da kwamitin binciken Magu
EFCC: ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji bada gudunmawar karya
Abinda yasa EFCC zata binciki Kwankwaso da wasu mutane
Wani abin duba game da hukumar ta EFCC shi ne ba a taba sanya shugaba an rabu lafiya tare da shi ba, Shugaban hukumar na farko Malam Nuhu Ribadu ba a yi rabuwar kirki da shi ba, domin kuwa karshe an rabu baram-baram ne.
Uwargida Farida Waziri ce ta gaje shi, wacce a lokacin da take shugabancin hukumar ta taba nemar cewa a rika yiwa ‘yan siyasa gwajin kwakwalwa saboda tsabar satar da suke yi ya wuce kima, ita ma dai an rabu da ita a hukumar dutse a hannun riga.
Shi kuwa Ibrahim Lamurde da ya gaje ta, har zuwa yanzu ba a san musabbabin abinda ya koreshi daga ofis ba.
Ga shi shima Ibrahim Magu yadda take kayawa a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login