Labaran Wasanni
Mari Market Cup: Layin Sabo Currency ya yi kunnan doki da FC Tasha
A ci gaba da gasar cin kofin kasuwar Mariri Mai taken Mariri Cola nut Market Cup da ake Kira da Chairman Cup.
A wasan da aka buga a ranar Lahadi 26 ga watan Satumbar shekarar 2021, tsakanin kungiyar Layin Bashir Sabo Currency da FC Tasha an ta shi wasa kunnan Doki kowanne layi na da kwallo 1 a zare, wanda hakan yasa aka tashi da ci 1-1.
Dan wasan Layin Sabo Currency ne ya fara zura kwallo a mintuna na 18, inda dan wasan FC Tasha ya farke kwallon a mintuna 60 da wasan.
Da yake jawabi bayan kammala wasan mai horas da ‘yan wasan kungiyar Layin Sabo Currency Musbahu Abdullahi Muhammad ya ce “kurakuran da ‘yan wasan mu suka samu shi yasa aka warware kwallo1 da muka saka a zare, amma muna sakaran samun nasara a wasan da zamu buga nan gaba”.
Shima mai horas da ‘yan wasan FC Tasha Muhammad Yahaya da ake Kira da (Tarago) ya ce “ba karamin kokari ‘yan wasanmu su ka yi ba wajen warware kwallon da aka sa mana a zare”.
Za’a ci gaba da gasar a ranar Juma’a 1 ga watan Oktobar shekarar 2021.
Tsakanin Layin Sunusi Dan Mande da Layin ‘Yan Bage da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar.
You must be logged in to post a comment Login