Labarai
Masarautar Rano ta naɗa sabbin Dagatai da ma su unguwanni

Masarautar Rano ta naɗa sabbin Dagatai bakwai, ciki har da masu unguwanni biyu da Malami ɗaya da aka ɗaga darajarsu zuwa Dagatai.
Wannan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran Masarautar, Malam Nasiru Habu Faragai, ya fitar.
Ya ce, daga cikin waɗanda aka ɗaga darajarsu akwai Alhaji Gali Ado a matsayin sabon Dagacin Bul da Alhaji Abdullahi Bono a matsayin Dagacin Karwai, yayin da Alhaji Abubakar Adamu ya zama sabon Dagacin Sabaru.
Sanarwar ta ce, Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umar, ya bayyana cewa an gudanar da naɗin ne domin inganta shugabancin al’umma da kusantar da masarautar ga jama’a, tare da buƙatar sabbin Dagatan su riƙe amanar da aka ɗora musu bisa gaskiya da tsoron Allah.
Haka kuma, Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Naziru Ya’u Rano, da Mataimaki na Musamman ga Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, Ado Yahaya Panda, sun yi magana kan muhimmancin naɗin, yayin da sabbin Dagatan suka yi alƙawarin gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da kare haƙƙoƙin al’ummomin su.
You must be logged in to post a comment Login