Labarai
Sarkin Rano ya ɗaga darajar Dagatai biyu zuwa Hakimai

Majalisar masarautar Rano ta daga darajar Dagacin Fammar Alhaji Isma’ila Usman Fammar zuwa Hakimin gundumar Fammar da kuma Dagacin Dunkuran Durba Alhaji Nura Abdulkadir Ja’e zuwa Hakimin gundumar Dunkuran Durba da ke yankin ƙaramar hukumar Kibiya.
Mai Martaba Sarkin Rano Ambassada Dakta Muhammad Isa Umar ya bayyana hakan ne a zaman majalisar masarautar karo na tara 9 wanda aka gudanar a fadar Mai Martaba Sarkin da ke sabon garin rano.
Sarkin na Rano ya ce, Sauran batutuwan da majalisar masarautar ta amince dasu a zaman sun hada da raba yankin dagacin garin rano zuwa dagatai biyu dagacin fuskar arewa da Kuma dagacin fuskar kudu Sai Kuma raba garin dagacin bunkure zuwa dagatai biyu wato dagacin fuskar bunkure ta arewa da dagacin bunkure ta fuskar kudu San nan Kuma zaman ya amince da raba kasar dagacin Kahu zuwa dagatai biyu dagacin Kahu da Kuma dagacin Falangai.
Sanarwar da sakataren Yada Labaran masarautar ta rano Nasiru Habu Faragai ya fitar ta kara da cewar zaman majalisar ya amince da sake duba yiwuwar farfado da garuruwan dagatai talatin da biyar da aka hade su da wasu garuruwan a shekarun baya sakamakon gazawar da dagatan wancan lokutan sukai na tattaro kudaden haraji.
Daga nan ne Mai Martaba Sarkin na rano Ambassada Dakta Muhammad Isa Umar ya yabawa gwamna injiniya Abba Kabir Yusuf bisa amincewar masarautar ta rano ta kirkiro Karin Sabbin gundumomi hakimai Sha biyar Wanda hakan ya bada damar samun wannan cigaba.
You must be logged in to post a comment Login