Labarai
Masu bukatar a raba kasar nan 2 za su fi kowa shiga tsaka mai wuya – Lai Muhammad
Gwamnatin tarraya ta bukaci al’ummar kasar nan da su yi watsi da maganganun raba kasar nan gida biyu.
Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed ne bayyana hakan a wata hira da gidan Radiyo a Lagos.
Alhaji Lai Muhammad y ace, idan aka raba kasar nan gida biyu kamar yadda wasu ke bukata, to kuwa za’ a shiga cikin tsaka mai yuwa.
Ya ce, wadanda ke neman a raba kasar su za sufi shiga tashin hankali sannan su bar kasar ba tare da sun shirya ba.
Ministan ya kara da cewa, idan har basu bada hadin kai wajen farfado da kasar nan ba, to kuwa bai kamata a riga ikirarin cewa a rabata ba.
You must be logged in to post a comment Login