Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Masu cutar Corona 187 suka rage a Kano

Published

on

Gwmanatin jihar Kano ta ce zuwa yanzu mutum 187 ne suka rage cikin masu jiyyar cutar Corona a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta sanar a ranar Litinin ta shafinta na Twitter cewar, an yiwa mutane 128 gwajin Corona a jihar, kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa dukkan su ba sa dauke da cutar.

Mutum 1,268 ne dai ma’aikatar lafiya ta Kano ta tabbatar da cewa sun kamu da cutar, cikin mutane 14,448 da aka yiwa gwajin cutar a jihar.

1,029 daga cikin masu cutar sun warke, sai mutum 52 da suka rasu sanadiyyar cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!