Labarai
Masu dauke da cutar HIV a Kano sunyi zanga -zanga
A jiya ne masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki HIV/AIDS sukayi zanga-zangar lumana domin nuna rashin gamsuwa da irin kyamata da tsangwama da al’umma da gwamnatani ke nuna musu.
Wasu daga cikin masu dauke da wannan cuta sunyi kira ga gwamnati da ta basu aikin yi domin wasu daga cikinsu sunyi karatu kuma suna da yara da suke kula dasu.
SACA: kimanin kaso 35 cikin dari masu dauke da cutar HIV ke karbar magani
Gwamnatin Najeriya zata dauki masu kwarewa a fannin koyarwa
Matan kuma sun bayyana cewa mazajensu basa zama da su idan suka gano suna dauke da wannan cuta mai karya garkuwar jiki.