Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masu garkuwa da mutane sun ɓulla a Kano

Published

on

Wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari a dajin Falgore, kan hanyar ƙaramar hukumar Doguwa zuwa birnin Kano.

Wani shaidar gani da ido mai suna Ado Musa mazaunin garin na Doguwa ya shaidawa Freedom Radio cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na safe, inda masu garkuwar ɗauke da makamai suka tsare kan titi tare da kama mutane.

Ado Musa ya ƙara da cewa lamarin ya rutsa da wasu mutane uku da har zuwa yanzu ba a san inda suke ba, sai kuma wasu da suka jikkata a yayin afkuwar lamarin.

Daga cikin waɗanda suka tsira da raunuka akwai kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Doguwa Malam Mukhtar Abdulmumin wanda lamarin ya rutsa da shi a kan hanyar sa ta zuwa Kano, inda yanzu haka yake ci gaba da samun kulawa a asibiti kamar yadda babban kwamandan Hisbah na jiha Sheikh Harun Ibn Sina ya shaidawa Freedom Radio.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin, har ma ya ce, tuni suka fara bincike a kai.

Labarai masu alaƙa:

An umarci ‘yan sanda su zama cikin shirin kota kwana a Kano

Ganduje zai mayar da dajin Falgore wurin atisayen sojoji

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!