Labarai
Masu garkuwa sun kashe wani ƙaramin yaro a Kano
Masu garkuwa da mutane sun hallaka wani ƙaramin yaro Hamza Ibrahim a ƙaramar hukumar Doguwa da ke nan Kano.
Mahaifin yaron Ibrahim Doguwa ya shaida wa Freedom Radio cewa, baya gari aka kira shi a waya aka sanar da shi ɓatan yaron.
Daga baya kuma sai ya samu wata wayar inda suka nemi da ya biya kuɗin fansa har miliyan 20.
Sai dai hakan bai samu ba, kuma suka hallaka yaron.
Kakakin ƴan sandan Kano SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin.
Kiyawa sun cafke waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, kuma maƙwabtan gidansu yaron ne.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Abduljalal Mas’ud Ƴantama, da Fadda Dahiru Ƴan Tama da Adam Ibrahim sai kuma Bashir Mai niƙan Shinkafa.
You must be logged in to post a comment Login