Kaduna
Rana zafi : Ƴan shara sun shiga yajin aiki a Kaduna
Masu kwashe shara sun tsunduma ya jin aiki a jihar Kaduna sakamakon rashin biyansu haƙƙoƙinsu da kamfanin lura da kwashe shara a jihar ya yi.
Hannatu Yusuf na daga cikin masu kwasar shara a mazaɓar Yalwa da ke ƙaramar hukumar Chukun ta shaida wa Freedom Radio cewa sun shafe tsawon lokaci ba tare da an biya su haƙƙoƙinsu ba.
Shi ma Abdullahi Abubakar da ke kwashe shara a mazaɓar Kaduna ta Arewa ya ce, tun kafin daina biyansu haƙƙoƙinsu, suna fama da matsalar zaftare musu kuɗaɗensu ba tare da wani dalili ba.
Freedom Radio ta tuntuɓi Alhaji Ashiru Sani Hussain ɗaya daga cikin shugabannin gudanarwa na kamfanin Cape-Gate da ke lura da kwashe shara a jihar Kaduna wanda ya ce, suna iya ƙoƙarinsu don magance matsalar amma lamarin ya fi ƙarfinsu, a don haka su ke neman agaji daga gwamnatin jihar Kaduna kan ta shiga tsakanin kamfanin da ma’aikatar muhalli ta jihar Kaduna.
Wakilinmu Haruna Ibrahim Idris ya rawaito mana cewa al’umma a birnin Kaduna sun lura da yadda ma’aikatan kwasar sharar suka ƙauracewa ayyukan su, lamarin da ya fara ta’azzara yawaitar shara a yankunan jama’a.
Al’umma su guji zuba shara a magudanan ruwa – REMASAB
Tsafta muka fi baiwa fifiko a sana’ar mu –Masu lemo da Mangwaro
Rahoto : Yadda tsaftar mahalli na ma’aikatu da kasuwanni ya kasance a Kano
Sai ku biyo mu nan gaba don jin matsayar ma’aikatar muhalli ta jihar Kaduna da kuma gwamnatin jihar.
You must be logged in to post a comment Login