Labarai
Masu laifi da ke buƙatar yafiya sun kai 320 a ƙasar nan – Abubakar Malami
Ministan shari’a kuma antoni janar na ƙasa Abubakar Malami ya ce, ma’aikatar shari’a ta karbi buƙatu 320 a madadin wasu da aka yanke wa hukuncin kisa da ke bukatar neman afuwar shugaban kasa.
Malami ya yi wannan bayani ne a lokacin a taron kwamitin ba da shawara na shugaban kasa kan hakkin bada afuwa ga masu laifi.
A cewar Malami, tun lokacin da kwamitin ya gabatar da rahotonsa kuma ya ci gaba da hutu, ma’aikatar ta samu takardun buƙatu masu yawa na neman yafiya daga wajen shugaban kasa.
Malami ya kuma ce, ya zama wajibi kwamitin ya dawo bakin aiki, la’akari da yadda bukatar neman yafiya a wajen shugaban kasa yayi yawa daga wadanda aka yanke wa hukuncin kisa a kasar nan.
Ministan ya tabbatar da cewa kwamitin zai duba buƙatu guda 320 da ofishinsa ya karba zuwa yanzu kuma zai ba da shawara kamar yadda ya dace dangane da yin yafiyar.
You must be logged in to post a comment Login