Labaran Kano
Masu suyar Kosai za su fara biyan haraji a Kano
Jama’ar da ke gudanar da kananan sanao’i da suka yi rumfa ko suka ajiye kwantaina a yankin karamar hukumar Birnin Kano da kewaye, za su fara biyan wani tsarin harajin kasa wato “Temporary shed/stand permit”.
A cikin wata takarda da wasu jami’ai su ka rika rarrabawa ga masu kwantainoni da rumfuna a unguwar Tukuntawa dake karamar hukumar ta birni, ta nuna cewa duk wani mai Kwantaina ko wanda yayi rumfa yana sayar da kaya zai biya kudi har naira dubu biyar cikin wa’adin kwanaki bakwai.
A cewar takardar duk wanda ya gaza biyan kudin cikin wa’adin na kwanaki bakwai majalisar karamar hukumar tana da ‘yancin daukar mataki akansa wanda zai kai ga rushe wajen sana’ar ta sa.
Wasu jami’an da ke raba takardun ga masu rumfunar sun shaidawa Freedom Radio cewa wannan umarni ne daga karamar hukumar Birnin Kano.
To sai dai Freedom Radio ta ziyarci sakatariyar karamar hukumar ta Birni don fayyace gaskiyar lamarin, to amma jami’an da ke sashen sun shaida mana cewa ba za su iya cewa komai ba akan batun, sai dai a garzaya wani ofishi da ke unguwar Sharada akwai wani jami’i mai suna Sabo shi ya ke da alhakin wannan lamari.
Sai dai bayan Freedom Radio ta ziyarci ofishin da ke Sharada nan ma jami’an wajen sun ce babu wani jami’in su mai wannan suna Kuma hasalima su ba su san da wannan batu ba domin ba aikinsu bane.
Ku cigaba da bibiyar Freedom Radio domin jin labarai da rahotonni na musamman.
You must be logged in to post a comment Login