Labarai
Matasa su rungumi Kasuwancin Internet -Dakta Kabiru Sufi
Malami a kwalejen ilimi da share fagen shiga jami’a ta Kano CAS Dokta Kabiru Sufi, ya ce matasa na da damar samarwa kansu ayyuka da sana’o’i, matukar suka yi amfani da kafafen sadarwa na intanet wajen gudanar da kasuwancin zamani.
Dokta Kabiru Sufi, ya bayyana haka ne yau yayin wani taron karawa juna sani da cibiyar PR Nigeria tare da hadin gwiwar gidauniyar tunawa da Habiba Jimeta suka shiryawa ‘yan jarida, kan yadda za a yi amfani da kafafen sadarwa na zamani a wannan hali da ake ciki na fama da cutar Corona.
Labarai masu alaka.
Ana tafka kurakurai wajen amfani da Internet- kungiyar Smart Clicks
Matar da ta makance sakamakon kashe ‘’yayanta sojoji biyu ta samu taimako ta kafar sada zumunta
Dakta Kabiru Sufi, ya ce duk da kalubale da ake fuskanta a sadarwa ta Zamani , kafafen sadarwar wata dama ce ta samar da hanyoyin bunkasa kasuwanci ba tare da haduwa da juna ba, ta hanyar zaurukan tallata kaya.
A na sa jawabin ya yin taron shugaban cibiyar PR Nigeria Adnan Mukhtar Tudunwada, ya ce sun shirya taron ne musamman ga ‘yan jarida kasancewar su jakadun al’umma, tare da wayar da kan matasa wajen amfana da kafafen sadarwar.
Masana da dama ne suka gabatar da makala kan yadda za a yi amfani da kafafen sadarwar na zamani wajen kasuwanci da yadda za a kaucewa kalubale, g dimbin matasan da suka halarci taron na yau.
You must be logged in to post a comment Login