Labarai
Matashin da ya mayar da wayar dubu 60 da ya tsinta a Kano
Wani matashi mai suna Abdurrahman Abdulkarim ya mayar da wayar salula da ya tsinta ta kimanin Naira dubu sittin.
Matashin ɗan unguwar Fagge ne, kuma ɗalibi a makarantar Sakandire ta Ƙofar Nassarawa.
Abdurrahman ya shaida wa Freedom Radio cewa, ya tsinci wayar ne a baburin adaidata sahu.
Daga nan ne kuma suka riƙa waya da mai wayar har ya tafi ya same shi domin mayar masa da wayarsa.
Ya ce “Idan na riƙe wayar ba abin da za ta ƙaramin domin ba tawa ba ce, shi yasa na ga bani da zaɓi fa ce na mayar masa”.
“A baya ma na taɓa tsintar waya ta wani dattijo, kuma na mayar masa”.
Shi ma a nasa ɓangaren mamallakin wannan waya Alhaji Bala Muhammad Nasir, ya yi wa matashin godiya tare da ba shi tukuici.
Ya ce “Na yi farin ciki matuƙa da irin nagartar da wannan matashi ya nuna, tabbas abin a yaba masa ne”.
Babban Kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Ustaz Muhammad Haruna Ibn Sina ya jinjinawa iyayen wannan matashi.
Ya ce, babu shakka iyayen sun yi abin ƙwarai wajen tarbiyyar ƴaƴansu.
Ibn Sina ya yi kira ga sauran jama’a da su yi koyi da irin kyawun halin da Abdurrahman ya nuna.
You must be logged in to post a comment Login