Labarai
Matawalle ga ‘yan kudu: Idan ‘yan arewa suka kai harin ramuwa ba za mu iya kareku ba
Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammed Matwalle ya yi gargadin cewa al’ummar arewa za su iya mai da martani matukar aka ci gaba da kashe ‘yan yankin a kudancin kasar nan.
Ya kuma bukaci takwarorin-sa na kudu da su dakatar da faruwar lamarin don gudun harin daukar harin ramuwa a arewa.
Gwamnan na Zamfara ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daidai lokacin da kungiyar dattijan arewa ta ACF ta fitar da makamancin sanarwar da ke sukar shugabannin kudanci kan shiru da su ka yi ana kashe al’ummar arewa a yankin su.
Gwamnan na Zamfara ta cikin sanarwar dai, ya kuma ce, rayuwa da dukiyar al’ummar arewa na fuskantar barazana daga al’ummomin kudanci, wadanda ke cin zarafinsu a ko da yaushe.
Bello Muhammed Matawalle ya kuma ce wannan ba lokaci bane da za ayi amfani da siyasa, amma lokaci ne da ya zama wajibi mu gayawa kanmu gaskiya domin halin da ake ciki abin damuwa ne.
You must be logged in to post a comment Login