Kiwon Lafiya
Matuƙar ba ku yi aiki ba, ba za mu biya ku albashi ba – Gwamnatin tarayya ga ƙungiyar NARD
Gwamnatin tarayya ta ce, ba za ta ci gaba da biyan ma’aikatan ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa albashi ba matuƙar suna cikin yajin aikin a yanzu.
Ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan yayin taron ministoci na mako-mako.
Ya ce, hukuncin da aka yanke ya zama wajibi domin kuwa yajin aikin da suka tafi ba shi da tushe ballanta makama.
Ehanire ya ce, ƙungiyar ƙwadago ta duniya ta amince da irin wannan mataki na rashin biyan ma’aikata albashi matuƙar ba su yi aikin su ba.
Ministan lafiyar ya ce, yanzu haka gwamnatin tarayya ta maka ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewar a gaban kotun ma’aikata, kan cewa babu dalilin da zai sa gwamnati ta biya su albashi alhalin ba sa aiki a lokacin.
You must be logged in to post a comment Login