Labarai
Mawaƙi Rarara ya yi hatsarin Mota
Fitaccen mawaƙin siyasa kuma shugaban kungiyar ƴan Kannywood ta 13X13, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya yi hatsarin mota.
Mai magana da yawun mawakin, Rabiu Garba Gaya ne ya sanar a safiyar Juma’a cewa Rarara ya yi hatsarin ne a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama, amma bai bayyana ko a ina ba ne.
A sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Facebook, hadimin a Raraya ya dora hotunan yada motar mawakin ta fada a cikin wata katuwar kwata da kuma yadda gaban motar ya yi kaca-kaca.
Sai dai ya bayyana cewa, duk da hatsarin, Raraya yana cikin koshin lafiya.
You must be logged in to post a comment Login