Labaran Wasanni
Mikel Arteta ka iya rasa aikin sa idan Arsenal ta yi rashin nasara a wasanni uku masu zuwa
Mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta, zai iya rasa aikin sa na horas da kungiyar, matukar tawagar bata yi nasara a wasanni uku da za ta buga nan gaba, a gasar premier kasar Ingila ba.
Arsenal dai za ta fafata wasan ta na gaba da Manchester City a ranar 28 ga watan da muke ciki na Agusta inda a ranar 11 ga watan Satumba za ta yi da Norwich City sai kuma a ranar 18 ga satumbar ta yi da Burnley
Tawagar ta Arsenal “tana mawuyacin halin da ba ta taba shiga makamancin sa ba bayan da ta fara kakar Premier League ta bana ba da karsashi ba” inji Mikel Arteta.
Kungiyar dai ta yi rashin nasara da ci 2-0 a gidan Brentford a wasan farko da ta yi kana ta sake rashin galaba a hannun Chelsea itama da ci 2-0 a karawar mako na biyu.
You must be logged in to post a comment Login