Labaran Wasanni
Mikel zai dawo taka leda a firimiyar Ingila
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles da Chelsea mai shekaru 33, Mikel Obi zai dawowa kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion ta kasar Ingila akakar wasa ta badi.
Kungiyar dai ta West Brom ta samu zarafin zuwa gasar firimiyar ta bane ne bayan da ta kasance daya daga cikin kungiyoyi ukun farko daga gasar Championship sai dai har zuwa yanzu ba’a tsayar da yarjejeniya tsakanin dan wasan da kungiyar ba.
Ajiya ne Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta West Brom, Slaven Bilic ya shaidawa manema labarai a birnin Landan cewa idan Dan wasan Mikel ya amince da dawowa kungiyarsa, babu shakka kungiyar za ta taka rawar gani a gasar ta firimiyar badi.
Ya zuwa yanzu dai bayan kungiyar kwallon kafan ta West Brom babu wata kungiya da ta nuna sha’awar daukar dan wasan tun bayan da al’amuran kwallon kafa suka faro dawo dai-dai sakamakon annobar Coronavirus.

You must be logged in to post a comment Login