Addini
Ministan birnin tarayya ya hana sallar idi a masallacin idi sai dai ayi a masallatan juma’a
Ministan birnin tarayya Abuja Muhammad Bello ya ba da umarnin haramta yin sallar idi a babban masallacin idi da ke titin Umaru Yar’adua da ke birnin sai dai a gudanar da sallar ta bana a masallatan juma’a.
Ya ce daukar matakin ya biyo bayan shawara da jami’an lafiya na birnin su ka bayar don rage cakuduwan jama’a wanda hakan wani mataki ne na kare kai daga yaduwar cutar corona
Muhammad Bello ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke ganawa da wata tawagar limamai karkashin jagorancin Imam Tajudeen Adigun wadanda suka kai masa ziyara ofishinsa
Ministan ya kuma shawarci limaman da su gudanar da sallar idi a masallatansu na juma’a
You must be logged in to post a comment Login