Connect with us

Labarai

Sojoji sun kashe yan ta’adda 152 tare da kama wasu 142

Published

on

Rundunar Operation Hadin Kai ta ce dakarunta sun halaka ’yan ta’adda 152, tare da kama wasu 142, yayin da 219 suka mika wuya a ayyukan da aka gudanar a arewa maso gabashin kasar nan cikin watan Agusta na shekarar 2026.

Ta cikin wata sanarwa rundunar ta ce ta kuma kai hare-haren sama 10, tare da lalata wasu bama-bamai tara na IED.

Haka kuma, sojojin sun kwato makamai da abubuwan fashewa 58, da harsasai 1,184, baya ga wasu kayan aiki da ake zargin ’yan Boko Haram da ISWAP ne ke amfani da su.

Rahoton ya ce an gudanar da ayyukan ne ta hanyar hare-haren kasa da sama, tattara bayanan sirri da kuma karfafa masu tayar da kayar baya su mika wuya, domin rage karfinsu da kuma dakile hanyoyin samun kayan aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!