Labarai
Ministan shari’a ya amince da halartar zaman kwamitin bincike na majalisar wakilai
Ministan shari’a na Nijeriya Abubakar Malami SAN, ya amince da halartar zaman kwamitin bincike na majalisar wakilai kan yadda aka sayar da ganga miliyan 48 ta danyen man fetur ba bisa ka’ida ba a shekarar 2015.
Shugaban kwamaitin binciken Mark Gbillah, ne ya sanar da hakan ga manema labarai jiya Alhamis a birnin tarayya Abuja.
Ya ce, Ministan zai bayyana a gaban kwamitin a ranar 27 ga wannan watan da muke ciki na Afirilu.
Mark Gbillah ya kara da cewa kwamitin ya gano yadda Abubakar Malami ya karbi wasu kudade daga kasashen ketare ba bisa tsarin nan na bayar da lada ga masu kwarmata bayanan sirri game da cin hanci da rashawa ba.
Ya kara da cewa bincikensu ya gano cewa ministar kudi Zainab Ahmad ce ta sahale biyan kudin.
You must be logged in to post a comment Login